2 Samuel 19:37 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka bar bawanka yă koma, don in mutu a garina, kusa da kabarin mahaifina da mahaifiyata. Amma ga bawanka Kimham. Bari yă ƙetare tare da ranka yă daɗe, sarki. Ka yi abin da ka ga dama da shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيَرْدَ مِنِ إِنْكُواْمَ دُواْمِنْ إِنْمُتُ عَثِكِنْ بِرْنِنَ كُسَدَ كَبَرِنْ بَابَنَ دَ مَامَاتَ؞ عَمَّا رَنْكَيَدَطٜىٰ، غَا بَاوَنْكَ طَانَ كِمْهَمْ؞ بَرِ يَتَڢِے تَرٜىٰدَكَيْ؞ كَيِمَسَ دُكْ أَبِنْدَ يَيِ دَيْدَيْ أَعِدُوانْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ina roƙonka ka bar ni in koma domin in rasu a garinmu, kusa da kabarin mahaifina. Amma ga Kimham barana, bari ya tafi tare da kai, ranka ya daɗe. Ka yi masa yadda kake so.”