2 Samuel 19:41 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nan take sai ga mutane Isra’ila suna zuwa wurin sarki, suna cewa, “Don me ’yan’uwanmu, mutanen Yahuda, suka saci sarki, suka kawo shi da iyalinsa a ƙetaren Urdun, tare da dukan mutanensa?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَجٜىٰ وُرِنْ سَرْكِے سُكَثٜىٰ مَسَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، مٜىٰيَسَا یَنْعُوَنْمُ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَ سَاثٜىٰكَ سُكَ ڧٜىٰتَرٜىٰ دَكَيْ دَ عِيَلِنْكَ دَ كُمَ مُتَنٜىٰنْكَ ذُوَا وَنَّنْ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dukan mutanen Isra'ila suka zo wurin sarki, suka ce masa, “Me ya sa mutanen Yahuza 'yan'uwanmu, suka sace ka, suka kawo sarki da iyalinsa a wannan hayin Urdun, tare da dukan mutanensa?”