2 Samuel 19:42 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan mutanen Yahuda suka ce wa mutanen Isra’ila, “Mun yi haka domin sarki danginmu na kurkusa ne. Don me kuke fushi game da wannan? Mun ci wani abu daga cikin kayan sarki ne? Mun ɗauki wani abu wa kanmu ne?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَثٜىٰ «مُنْيِ حَكَ غَمَا سَرْكِے طَنْعُوَنْمُ نٜىٰ نَثِكِنْمُ؞ دُوانْمٜىٰ كُكٜىٰ ڢُشِے غَمٜىٰدَ وَنَّنْ؟ أَيْ، بَا عَبِنْثِ كُواْ وَنِ أَبُ يَبَامُبَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan mutanen Yahuza suka amsa wa mutanen Isra'ila suka ce, “Domin sarki ɗan'uwanmu ne na kusa. Me ya sa kuke fushi a kan wannan al'amari? Me muka ci a jikin sarki, ko kun ji ya ba mu wani abu ne?”