2 Samuel 19:43 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan mutanen Isra’ila suka ce wa mutanen Yahuda, “Muna da rabo goma a wurin sarki; ban da haka ma, muna da hakki mafi yawa a wurin Dawuda fiye da ku. Don me kuke mana reni? Ba mu ne ma muka fara magana dawowa da sarki ba?” Amma mutanen Yahuda suka ɗauka maganar da zafi fiye da mutanen Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ أَمْسَوَ نَ يَهُودَ سُكَثٜىٰ «مُو ذُرِيَ غُواْمَ نٜىٰ أَمُلْكٍ؞ مُنَدَ إِيكُوانْ طَوْكَرْ دَاوُدَ يَذَمَ سَرْكِے ڢِيٜىٰ دَكُو! دُوانْمٜىٰ كُكَ رٜىٰنَمُ، كُواْدَيَكٜىٰ مُونٜىٰ مُكَ ڢَارَ ذَنْثٜىٰنْ دَاوُاْ دَ سَرْكِے؟» عَمَّا مَغَنَرْ دَ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ سُكَيِ تَاڢِے تَمُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Isra'ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?” Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra'ila zafi.