2 Samuel 19:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Yowab ya shiga gidan sarki ya ce, “Yau ka kunyatar da dukan mutanenka, waɗanda ba da daɗewa ba sun ceci ranka, da rayukan ’ya’yanka maza, da na ’ya’yanka mata, da na matanka da kuma na ƙwarƙwaranka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُواْوَبْ يَشِغَ غِدَنْ دَ سَرْكِے يَكٜىٰ يَثٜىٰمَسَ «يَوْ كَا كُنْيَتَرْدَ سُواْجُواْجِنْكَ؞ سُونٜىٰ سُكَثٜىٰثِ رَنْكَ دَ رَايُكَنْ یَیَنْكَ مَظَا دَ مَاتَادَ نَمَاتَنْكَ دَ كُمَ نَمَاتَنْدَ كَأَجِيٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yowab kuwa ya tafi wurin sarki a gidansa ya ce, “Yau ka kunyatar da mutanenka duka waɗanda suka ceci ranka, da rayukan 'ya'yanka mata da maza, da rayukan matanka, da rayukan ƙwaraƙwaranka.