2 Samuel 19:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kana ƙaunar maƙiyinka, kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Ka bayyana a fili cewa komandodi da sojojinsu ba kome ba ne a gare ka. Na ga cewa da za ka yi farin ciki, da a ce Absalom yana da rai a yau, dukanmu kuma mun mutu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَڢِ سُوانْ وَطَنْدَ سُكٜىٰڧِنْكَ، سَعَنً كَنَڧِنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰسُوانْكَ؞ يَوْ كَا نُونَ أَ ڢِيلِ ثٜىٰوَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ دَ سَوْرَنْ سُواْجُواْجِ بَكُواْمٜىٰبَنٜىٰ أَوُرِنْكَ؞ إِنَ غَنِ ذَاكَڢِے يِنْ مُرْنَ يَوْ دَا عَثٜىٰ أَبْسَلُوامْ يَنَدَ رَيْ عَمَّا دُكَنْمُ مُنْ مُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama kana ƙaunar maƙiyanka, amma kana ƙin waɗanda suke ƙaunarka. Gama yau ka bayyana a fili, shugabannin sojojinka da fādawanka ba a bakin kome suke a gare ka ba. Gama yau na gane da a ce Absalom yana da rai, mu kuwa muka mutu duka, da daɗi za ka ji.