2 Samuel 19:7 โ Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu ka fita ka ฦarfafa mutanenka. Na rantse da Ubangiji, in ba ka fita ba, babu mutum guda da za a bari tare da kai a daren nan. Wannan zai fi maka muni fiye da kowace irin masifar da ta auko maka tun ฦuruciyarka har zuwa yanzu.โ
Hausa Arabic 2020 (ุงููุชููููุฑูุชู ุฏู ุงูููููุจูุงููุง)
ููููุฐููููููุ ุณููู ููุชูุงุดู ฺููขูุชู ฺููงูุฑฺูขฺูขู ู
ูุชูููููฐููููุ ููุง ุถฺููููููฐ ุฏู ููููููููฐูู ุนูุฏููู ุจููู ฺขูุชูุจูุ ุจูุงุจู ู
ูุชูู
ู ุบูุฏูุง ุฏู ุฐููู ุถูุบูููฐ ุชูุฑูููฐุฏููููู ุงููุฏูุฑูููฐูููููุ ููููููู ุฐููู ููู
ููู ุฐูุงฺขู ฺขูููููฐุฏู ุฏููููู ูููููููุงูููููุฏู ฺููขูุณูููููุชู ุชููู ูููู ุณูููุฑููู ุญูุฑู ุฐูููุง ููููุยป
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka sai ka tashi yanzu, ka fita ka yi wa mutanenka magana mai daษi. Gama na rantse da Ubangiji idan ba ka fita ba, ba wanda zai zauna tare da kai da daren nan. Wannan kuwa zai fi muni fiye da kowane irin mugun abin da ya taษa samunka tun daga ฦuruciyarka har zuwa yanzu.โ