2 Samuel 19:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sarki ya tashi, ya zauna a bakin hanyar shiga. Da aka faɗa wa mutane cewa, “Sarki yana zaune a bakin hanyar shiga,” sai duk suka zo gabansa. Ana cikin haka, Isra’ilawa dai sun riga sun tsere zuwa gidajensu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، سَيْ سَرْكِے يَتَاشِ يَتَڢِے وُرِنْ تَارُوَ عَڧُواْڢَرْ غَرِ يَذَوْنَ؞ دَلَابَرِ يَبَظُو ثٜىٰوَ سَرْكِے يَنَ ظَوْنٜىٰ أَوُرِنْ ذَمَنْسَ عَڧُواْڢَرْ غَرِ، سَيْ دُكَنْ مُتَنٜىٰ سُكَ تَارُ وُرِنْسَ؞ أَنَ ثِكِنْ حَكَ سَيْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ سُكَبِے أَبْسَلُوامْ سُكَ غُدُ ذُوَا غِدَاجٜىٰنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan sarki ya tashi, ya zauna a dandalin ƙofar garu. Aka faɗa wa mutanensa duka, cewa, ga sarki yana zaune a dandalin ƙofar garu. Mutanensa duka kuwa suka zo suka kewaya sarki. Bayan wannan sai dukan Isra'ilawa suka gudu, kowa ya tafi gidansa.