2 Samuel 19:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutane ko’ina a kabilan Isra’ila, suka yi ta gardama da juna, suna cewa, “Sarki ne ya cece mu daga hannun abokan gābanmu, shi ne kuma ya kuɓutar da mu daga hannun Filistiyawa. Amma ga shi ya tsere daga ƙasar saboda Absalom;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْعِنَ عَثِكِنْ ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ مُتَنٜىٰ سُكَ شِغَ غَرْدَمَ دَ جُونَنْسُ سُنَ ثٜىٰوَ «سَرْكِے دَاوُدَ نٜىٰ يَثٜىٰثٜىٰمُ دَغَ حَنُّنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْمُ؞ شِينٜىٰ كُمَ يَكُٻُتَرْ دَمُو دَغَ حَنُّنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞ عَمَّا يَنْذُ يَغُدُ دَغَ ڧَسَرْ سَبُواْدَ أَبْسَلُوامْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan mutanen ƙasar Isra'ila suna ta jayayya, suna cewa, “Sarki Dawuda ne ya cece mu daga hannun abokan gabanmu, ya cece mu daga hannun Filistiyawa, to, ga shi, ya gudu daga ƙasar don ya tsere wa Absalom.