2 Samuel 2:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan kowannensu ya kama abokin gābansa a kā ya soki da wuƙa a jiki, sai duka suka fāɗi a ƙasa. Saboda haka ne ake kiran wannan wuri Helkat Hazzurim a Gibeyon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَنٜىٰ يَكَامَ أَبُواْكِنْ ڢَطَنْسَ عَكَيْ، يَسُواْكِ أَبُواْكِنْ ڢَطَنْسَ دَ تَكُواْبِے تَغٜىٰڢٜىٰنْ ثِكِنْسَ؞ دَ حَكَ سُكَ ڢَاطِ تَرٜىٰ، دُكَنْسُ سُكَ مُتُ؞ عَكَ سَا وَوُرِنَّنْ وَنْدَ يَكٜىٰ أَ غِبٜىٰيُوانْ سُونَ هٜىٰلْكَتْ هَڟُرِمْ، وَتُواْ ڢِيلِنْ تَكُواْبِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowa ya kama abokin kokawarsa a kā, suka soki juna a kwiɓi da takuba. Suka faɗi tare. Aka sa wa wurin suna Helkat-hazzurim, wato filin takuba, wurin yana nan a Gibeyon.