2 Samuel 20:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَمَسَ كُوَ بَيْ لُورَ دَ تَكُواْبِنْ دَيَكٜىٰ أَ حَنُّنْ هَغُنْ يُواْوَبْ بَ؞ تَهَكَ يُواْوَبْ يَسُواْكِ أَمَسَ دَ تَكُواْبِے عَثِكِ حَرْ كَايَنْ ثِكِنْسَ سُكَ ظُبَ ڧَسَا؞ أَمَسَ يَمُتُ بَاتَرٜىٰدَ يُواْوَبْ يَسُواْكٜىٰشِ سَوْ بِيُبَ؞ سَيْ يُواْوَبْ دَ طَنْعُوَنْسَ أَبِشَيْ سُكَ ثِيغَبَدَ بِنْ شٜىٰبَ طَنْ بِكِرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Amasa bai lura Yowab yana da takobi a hannunsa ba. Yowab kuwa ya kirɓa masa takobin a ciki sau ɗaya, sai hanjin Amasa ya zuba ƙasa, ya mutu. Sa'an nan Yowab da Abishai ɗan'uwansa suka bi sawun Sheba, ɗan Bikri.