2 Samuel 20:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amasa kuwa yana kwance cikin tafkin jininsa a kan hanya, sai mutumin ya ga dukan sojoji suka zo suka tsaya cik a can. Da ya gane cewa duk wanda ya haura zuwa wurin Amasa sai ya tsaya, sai ya ja gawar Amasa daga hanyar ya kai can cikin wani fili ya rufe shi da zane.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَمَسَ كُوَ يَݣُونْتَ عَثِكِنْ جِنِنْسَ أَڟَكِيَرْ حَنْيَ، كُمَ عِدَنْ كُواْوَ يَكَيْ وُرِنْ غَاوَرْ سَيْ يَڟَيَ يَيِ كَلُّواْ؞ دَ سُواْجَنْ يَغَ يَدَّ كُواْوَ يَكَنْ ڟَيَ أَوُرِنْ غَاوَرْ، سَيْ يَجَا غَاوَرْ دَغَ حَنْيَ، يَݣُونْتَرْدَ عِتَ عَثِيَوَ تَغٜىٰڢٜىٰنْ حَنْيَرْ، سَعَنً يَرُڢٜىٰتَ دَ رِغَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gawar Amasa kuwa ta birkiɗe da jini tana a tsakiyar hanya. Da mutumin ya ga yadda dukan mutane suka tsaya, sai ya kawar da ita daga tsakiyar hanya zuwa cikin saura, ya rufe ta da tufa, gama dukan wanda ya ga gawar, sai ya ja, ya tsaya.