2 Samuel 20:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَعَبِنْدَ نَكٜىٰ نٜىٰمَبَ كٜىٰنَنْ؞ عَمَّا أَݣَويْ وَنِ مُتُمْ مَيْ سُونَ شٜىٰبَ طَنْ بِكِرِ دَغَ تُدَّنْ يَنْكِنْ إِڢْرَيِمْ وَنْدَ يَڢَارَيِ وَ سَرْكِے دَاوُدَ تَاوَيٜىٰ؞ كُمِيڧَ مِنِ وَنَّنْ مُتُمْ؞ نِے كُوَ ذَنْ جَنْيٜىٰ دَغَ بِرْنِنْ؞» سَيْ مَثٜىٰنْ تَأَمْسَ مَسَ تَثٜىٰ «تُواْ، ذَاعَ جٜىٰڢَرْ مَكَ دَ كَنْ شٜىٰبَ تَكَتَنْغَرْ بِرْنِنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba haka ba ne, ni dai ina neman mutumin ƙasar tudu ta Ifraimu, wanda ake ce da shi Sheba, ɗan Bikri. Shi ne ya tayar wa sarki Dawuda. Shi kaɗai za ku ba ni, ni kuwa zan janye daga garin.” Macen kuwa ta ce wa Yowab, “To, za a jefar maka kansa ta kan garu.”