2 Samuel 20:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً مَثٜىٰنْ تَبِے دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِنْ تَيِ مُسُ مَغَنَ دَ حِكِمَرْتَ؞ سَيْ سُكَ يَنْكٜىٰ كَنْ شٜىٰبَ طَنْ بِكِرِ سُكَجٜىٰڢَوَ يُواْوَبْ تَكَتَنْغَرْ؞ دُواْمِنْ حَكَ يُواْوَبْ يَبُوسَ ڧَهُواْ دُواْمِنْ سُواْجُواْجِ سُجَنْيٜىٰ دَغَ بِرْنِنْ؞ كُواْوَنٜىٰ مُتُمْ يَكُواْمَ غِدَنْسَ، يُواْوَبْ كُوَ يَكُواْمَ وُرِنْ سَرْكِے أَ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.