2 Samuel 20:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ دَاوُدَ يَكُواْمَ غِدَنْسَ أَ عُرُوشَلِيمَ، سَيْ يَݣُوسُواْ مَتَنْ دَ يَأَجِيٜىٰ غُدَا غُواْمَ وَطَنْدَ يَبَرْسُ سُلُورَ دَ غِدَنْسَ؞ يَسَاسُ أَوَنِ غِدَا، يَكُمَسَا عَيِ غَادِنْسُ؞ يَثِيغَبَدَ بِيَنْ بُڧَاتُنْسُ، عَمَّا دَيْ بَيْ سَاكٜىٰ ݣُونَ دَسُوبَ؞ عَكَ ڨَلٜىٰسُ أَوُرِنْ حَرْ رَانَرْ مُتُوَرْسُ، سُكَيِ تَذَمَ كَمَرْ مَاتَانْدَ مَذَنْسُ سُكَ مُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Dawuda ya koma gidansa a Urushalima, kwarakwaran nan nasa guda goma waɗanda ya bar su tsaron gida ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya yi ta lura da su, amma bai shiga wurinsu ba. Haka suka zauna a keɓe, suna zaune kamar gwauraye.