2 Samuel 20:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ يُواْوَبْ دَ مُتَنٜىٰنْسَ دَ سُواْجُواْجِنْ دَسُكٜىٰ غَادِنْ سَرْكِے دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِ مَاسُ عِيَ يَاڧِ سُكَ بَرْ عُرُوشَلِيمَ تَرٜىٰدَ أَبِشَيْ؞ سُكَبِے شٜىٰبَ طَنْ بِكِرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan mutanen Yowab, wato Keretiyawa da Feletiyawa, da dukan jarumawa, suka bi bayan Abishai. Suka fita daga Urushalima don su bi sawun Sheba, ɗan Bikri.