2 Samuel 20:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَسُكَكَيْ وَنِ ڧَتُوانْ دُوڟٜىٰنْ دَيَكٜىٰ أَ غِبٜىٰيُوانْ، سَيْ أَمَسَ يَذُواْ يَسَدُدَسُو؞ يُواْوَبْ كُوَ يَنَ سَنْيٜىٰ دَ رِغَرْ سُواْجَ؞ عَكَنْ رِغَرْسَ كُمَ أَݣَويْ تَكُواْبِے عَثِكِنْ غِدَنْسَ طَوْرٜىٰ دَ طَمَرَ؞ دَ يَمَاڟَ غَبَ، سَيْ تَكُواْبِنْ يَڢِتَ يَڢَاطِ؞ يُواْوَبْ يَطَوْكَ دَ حَنُّنْ هَغُنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suke a babban dutsen Gibeyon, Amasa ya zo ya tarye su. A lokacin nan Yowab yana saye da rigar yaƙi, ya sha ɗamara, yana kuma rataye da takobi a ɗamararsa. Da ya gabato, sai takobin ya faɗi.