2 Samuel 21:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَتَڢِے وُرِنْ مُتَنٜىٰنْ يَبٜىٰشْ أَ غِلٜىٰيَدْ، يَسَا سُبَاشِ ڧَسُسُوَنْ طَالُوتَ دَ نَطَنْسَ يُواْنَتَنْ؞ تُنْدَا ثَنْ مُتَنٜىٰنْ يَبٜىٰشْ أَ غِلٜىٰيَدْ سُنْ سَاثِ غَوَوَّكِنْ طَالُوتَ دَ يُواْنَتَنْ دَغَ عِنْدَ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ كَكَّڢَسُ عَكَنْ إِتَاثٜىٰ أَ ڢِيلِ نَثِكِنْ غَرِنْ بٜىٰتْ شَنْ، بَايَنْدَ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ كَشٜىٰسُ عَبَبَّنْ تُدُنْ غِلْبُواْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda ya tafi ya kwaso ƙasusuwan Saul da na ɗansa Jonatan daga wurin mutanen Yabesh a Gileyad. (Gama suka sace su daga dandalin Bet-sheyan, a inda Filistiyawa suka rataye su, a ranar da suka kashe Saul a Gilbowa.)