2 Samuel 21:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya’are-Oregim mutumin Betlehem ya kashe Goliyat mutumin Gat, wanda girmar sandan māshinsa ta yi kama da taɓarya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ سَاكٜىٰيِنْ يَاڧِ دَ ڢِلِسْتِيَاوَا أَ غُوابْ؞ سَيْ عٜىٰلْهَنَنْ طَنْ يَايِرْ مُتُمِنْ بَيْتَلَحْمِ يَكَشٜىٰ طَنْعُوَنْ جَالُوتَ نَ غَتْ، وَنْدَ غِرْمَنْ سَنْدَنْ مَاشِنْسَ يَيِ كَمَ دَ تَٻَرْيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka sake yin yaƙi da Filistiyawa a Gab, sai Elhanan, ɗan Yayir, mutumin Baitalami, ya kashe ɗan'uwan Goliyat na Gat, wanda girman gorar māshinsa ta yi kama da dirkar masaƙa.