2 Samuel 21:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarki ya tattara Gibeyonawa ya yi musu magana. (To, Gibeyonawa ba sashen Isra’ilawa ba ne, amma mutanen Amoriyawa ne da suka ragu, waɗanda Isra’ila ta rantse za tă bari da rai, amma Shawulu cikin kishinsa don Isra’ila da Yahuda ya yi ƙoƙari yă hallaka su duka.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے دَاوُدَ يَكِرَا مُتَنٜىٰنْ غِبٜىٰيُوانْ يَيِ مَغَنَ دَسُو؞ سُو مُتَنٜىٰنْ غِبٜىٰيُوانْ كُوَ بَدَغَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ بَ، سُو مُتَنٜىٰنْ أَلْعُمَّنْ أَمُواْرِيَاوَا نٜىٰ دَسُكَ رَغُ؞ تُنْدَا إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُنْ ضَنْڟٜىٰ ثٜىٰوَ بَذَاسُ كَشٜىٰ مُتَنٜىٰنْ غِبٜىٰيُوانْ بَ؞ عَمَّا طَالُوتَ يَيِ ڧُواْڧَرِ يَكَشٜىٰسُ دُكَ سَبُواْدَ كِيشِنْ دَ يَكٜىٰدَشِ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ نَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
(Gibeyonawa dai ba mutanen Isra'ila ba ne, su Amoriyawan da suka ragu ne, waɗanda Isra'ilawa suka rantse musu, cewa, ba za su kashe su ba. Amma Saul, saboda kishin da yake yi domin mutanen Isra'ila da Yahuza, ya nema ya kashe su duk.)