2 Samuel 21:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
a ba mu zuriyarsa maza bakwai, mu kashe su, mu kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji a Gibeya na Shawulu wannan zaɓaɓɓen Ubangiji.” Sai sarki ya ce, “Zan ba ku su.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُمِيڧَ مَنَ یَیَنْسَ مَظَا بَݣَويْ؞ ذَامُ كَكَّشٜىٰسُ، مُكَكَّڢَ غَوَوَّكِنْسُ عَكَنْ إِتَاثٜىٰ أَ غِبٜىٰيَ، غَرِنْ طَالُوتَ، سَرْكِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَذَاٻَا؞» سَيْ سَرْكِے يَثٜىٰمُسُ «تُواْ، ذَنْ مِيڧَ مُكُسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ka ba mu 'ya'yansa maza bakwai domin mu rataye su a gaban Ubangiji a Gibeya a kan dutsen Ubangiji.” Sarki kuwa ya ce, “To, zan bayar.”