2 Samuel 21:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَمِيڧَسُ غَ مُتَنٜىٰنْ غِبٜىٰيُوانْ؞ سُو كُوَ سُكَ كَكَّشٜىٰسُ سُكَ كَكَّڢَ غَوَوَّكِنْسُ عَكَنْ إِتَاثٜىٰ عَبَبَّنْ تُدُ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ دُكَنْسُ بَݣَويْ طِنْ سُكَ مُتُ تَرٜىٰ؞ أَنْ كَكَّشٜىٰسُ أَ لُواْكَثِنْ دَ عَكَڢَارَ غِرْبِنْ حَڟِنْ بَلٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki kuwa ya bai wa Gibeyonawa su. Sai suka rataye su a kan dutse a gaban Ubangiji. Su bakwai ɗin nan suka hallaka gaba ɗaya. An kashe su a farkon kakar sha'ir.