2 Samuel 22:51 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَبَّرْ نَصَرَا يَكَنْ بَا سَرْكِنْدَ يَذَاٻَا، ڧَوْنَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا يَكَنْ نُونَ وَ وَنْدَ يَكٜىٰٻٜىٰ، غَ سَرْكِے دَاوُدَ دَ ذُرِيَرْسَ حَرْ أَبَدَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah ya ba sarkinsa manya manyan nasarori, Ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shi wanda ya zaɓa, Wato ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”