2 Samuel 23:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا سُونَيٜىٰنْ سُواْجُواْجِ مَڢِيَ عِيَ يَاڧِ سُواْسَيْ نَ دَاوُدَ؞ نَڢَرْكُواْ شِينٜىٰ يُواْشٜىٰبْ بَشّٜىٰبٜىٰتْ مُتُمِنْ تَكٜىٰمُوانْ، أَنْكُمَ سَنْشِ دَ سُونَ أَدِنُواْ عٜىٰظِنِ؞ شِينٜىٰ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ عُكُنَّنْ؞ يَتَٻَ طَوْكَرْ مَاشِنْسَ يَكَشٜىٰ مُتَنٜىٰ طَرِے تَݣُوسْ أَ لُواْكَثِ غُدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga sunayen jarumawan Dawuda, Yosheb-basshebet, daga Takemon, shi ne ɗaya daga cikin shugabanni uku. Ya girgiza māshinsa, ya kashe mutum ɗari takwas baki ɗaya.