2 Samuel 24:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ غَدْ يَذُواْ وُرِنْ دَاوُدَ يَثٜىٰ مَسَ «وَنّٜىٰ يَڢِ مَكَ، شٜىٰكَرَا عُكُ نَيُنْوَ عَڧَسَرْكَ؟ كُواْ وَتَا عُكُ نَغُدُ دَغَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكَ؟ كُواْ كُوَ ݣُونَ عُكُ نَبَلَعِ عَثِكِنْ ڧَسَرْكَ؟ تُواْ، سَيْ كَيِ تُنَانِ كَبَانِ أَمْسَرْ دَ ذَنْ كَيْوَ يَهْوٜىٰهْ ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”