2 Samuel 24:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، مٜىٰيَكَٰوُاْ سَرْكِے أَوُرِينَ؟» دَاوُدَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «نَا ذُواْ نٜىٰ إِنْ سَيِ وُرِنْ بُغُنْ حَڟِنْكَ إِنْ غِنَا بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ؞ أَ نَنْ ذَنْيِ هَدَايَ غَ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ يَڟَيَرْ دَ بَلَعِنَّنْ دَغَ كَنْ مُتَنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya ce, “Ranka ya daɗe, ya sarki, me ya kawo ka?” Sai Dawuda ya ce, “Don in sayi masussukarka ne domin in gina wa Ubangiji bagade, domin a kawar wa mutanen da annobar.”