2 Samuel 24:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْدَهَكَ سَرْكِے يَنَاثٜىٰ وَ يُواْوَبْ دَ سَوْرَنْ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ سُيِ بِيَيَّ دَ عُمَرْنِنْسَ؞ سَبُواْدَ حَكَ سُكَ تَڢِے دُواْمِنْ سُلِسَّڢْتَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma maganar sarki ta rinjayi ta Yowab da ta sauran shugabannin sojojin. Yowab kuwa da sauran shugabannin sojojin suka tashi daga gaban sarki suka tafi su ƙidaya mutanen Isra'ila.