2 Samuel 3:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبْنٜىٰرْ يَكُمَيِ مَغَنَ دَ ذُرِيَرْ بِلِيَامِنُ؞ سَعَنً يَتَڢِے وُرِنْ دَاوُدَ أَ هٜىٰبْرُوانْ دُواْمِنْ يَڢَطَا مَسَ ثٜىٰوَ يَيِݣَوْ أَعِدَانُنْ دُكَنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ دُكَنْ ذُرِيَرْ بِلِيَامِنُ سُغُواْيِ بَايَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Abner kuma ya yi magana da mutanen Biliyaminu, sa'an nan ya tafi ya faɗa wa Dawuda a Hebron abin da dukan Isra'ilawa da dukan kabilar Biliyaminu suka ga ya yi kyau, su yi.