2 Samuel 3:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَبْنٜىٰرْ يَثٜىٰ وَ دَاوُدَ «رَنْكَيَدَطٜىٰ! بَرِ إِنْ كُواْمَ إِنْ تَتَّارَ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذُوَا غَرٜىٰكَ، دُواْمِنْ سُيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَكَيْ، دُواْمِنْ كَاعِيَيِنْ مُلْكِ بِسَ دُكَنْ أَبِنْدَ رَنْكَ يَكٜىٰسُواْ؞» دَاوُدَ يَسَلَّمِ أَبْنٜىٰرْ، يَكُوَ تَڢِے لَاڢِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Zan tashi in tafi in tattara wa ubangijina sarki dukan Isra'ilawa, domin su yi alkawari da kai, kai kuma ka sarauce su yadda kake so.” Dawuda kuwa ya sallami Abner, ya tafi lafiya.