2 Samuel 3:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ أَلْحَكِنْ جِنِنْ أَبْنٜىٰرْ يَذَوْنَ عَكَنْ يُواْوَبْ دَ دُكَنْ غِدَنْ بَابَنْسَ! كَدَ كُواْوَثٜىٰ ڟَارَا أَ ذُرِيَرْسَ تَرَسَ مَيْ طِغَ، كُواْ مَيْ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے، كُواْ مَيْ جِنْغِنَ غَ سَنْدَا، كُواْ مَيْ رَوْنِ عَيَاڧِ، كُواْ مَيْ رَشِنْ عَبِنْثِ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.”