2 Samuel 3:39 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْدَيَكٜىٰ نِنٜىٰ سَرْكِنْ دَ اللَّهْ يَكٜىٰٻٜىٰ، دُكْدَهَكَ إِيكُواْنَ يَكَاسَ يَوْ؞ ذَاڢِنْ كَنْ یَیَنَّنْ نَ ظٜىٰرُوِيَ يَشَا مِنِ كَيْ؞ بَرِ يَهْوٜىٰهْ يَرَامَ وَمَيْ مُغُنْتَا بِسَغَ مُغُنْتَارْدَ يَعَيْكَتَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”