2 Samuel 5:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ دَاوُدَ يَتَمْبَيِ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ «كُواْ إِنْتَڢِے إِنْيَاڧِ ڢِلِسْتِيَاوَا؟ ذَاكَ بَاشٜىٰسُ أَ هَنُّونَ؟» يَهْوٜىٰهْ يَأَمْسَ «عِ، كَتَڢِے كَيَاڧٜىٰسُ؞ حَڧِيڧَ ذَنْ بَادَسُو أَ حَنُّنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”