2 Samuel 5:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْ لُواْكَثِنْ دَ طَالُوتَ يَكٜىٰ سَرْكِنْمُ، كَيْنٜىٰ كَكٜىٰبِے دَ إِسْرَٰٓءِيلَ عَيَاڧِ؞ يَهْوٜىٰهْ كُمَ يَغَيَ مَكَ ثٜىٰوَ كَيْنٜىٰ ذَاكَ ذَمَ مَكِيَايِنْ مُتَنٜىٰنْسَ إِسْرَٰٓءِيلَ، ذَاكَ كُمَ ذَمَ سَرْكِنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A dā sa'ad da Saul yake sarautarmu, kai kake bi da Isra'ilawa zuwa yaƙi, kai kake komo da su. Ubangiji kuma ya ce maka, ‘Kai za ka lura da jama'ata Isra'ila, za ka zama sarkinsu.’ ”