2 Samuel 5:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ دَاوُدَ يَتَڢِے بَعَلْ ڢٜىٰرَظِمْ، أَنَنْ يَثِ نَصَرَا عَكَنْ ڢِلِسْتِيَاوَا؞ سَيْ يَثٜىٰ « يَهْوٜىٰهْ يَا ٻَرْكٜىٰوَ أَبُواْكَنْ غَابَنَ كَمَرْ ضُوَنْدَ يَٻَرْكٜىٰ دَغَ دَمْ؞» سَيْ دَاوُدَ يَسَا وَوُرِنْ سُونَ بَعَلْ ڢٜىٰرَظِمْ، وَتُواْ عُبَنْ‌غِجِ يَٻَرْكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya zo Ba'al-ferazim, ya ci Filistiyawa a wurin. Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya huda abokan gabana a idona kamar rigyawa.” Saboda haka aka sa wa wurin suna, “Ubangiji Mai Hudawa.”