2 Samuel 5:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے دَاوُدَ دَ مُتَنٜىٰنْسَ سُكَ تَڢِے عُرُوشَلِيمَ دُواْمِنْ سُڢَاطَوَ يٜىٰبُسِيَاوَا مَذَوْنَنْ ڧَسَرْدَ يَاڧِ؞ سَيْ يٜىٰبُسِيَاوَنْ سُكَيِ وَ دَاوُدَ بَعَ سُكَثٜىٰ مَسَ «بَذَاكَ تَٻَ شِغَ نَنْبَ؞ كُواْ مَكَڢِ دَ غُرَغُ كَطَيْ مَا ذَاسُ كُواْرٜىٰكَ!» غَمَا سُنْيِ تُنَانِ ثٜىٰوَ دَاوُدَ بَذَيْ عِيَ شِغَ وُرِنْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Dawuda da mutanensa suka tafi Urushalima su yaƙi Yebusiyawa mazaunan ƙasar. Su kuwa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka iya zuwa nan ba, makafi kawai da guragu za su kore ka.” A zatonsu Dawuda ba zai iya zuwa can ba.