2 Samuel 6:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَݣُوتِ نَ يَهْوٜىٰهْ يَا ذَوْنَ أَغِدَنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ مُتُمِنْ غَتْ وَتَا عُكُ؞ يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَ أَلْبَرْكَثِ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ دَ دُكَنْ غِدَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwatin alkawarin Ubangiji yana a gidan Obed-edom Bagitte har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa Obed-edom da dukan iyalinsa albarka.