2 Samuel 6:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “ Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لَابَرِ يَكَيْ كُنّٜىٰنْ سَرْكِے دَاوُدَ ثٜىٰوَ يَهْوٜىٰهْ يَا أَلْبَرْكَثِ غِدَنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ دَ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰدَشِ تَدَلِيلِنْ عَݣُوتِنْ اللَّهْ ؞ سَيْ دَاوُدَ يَغَنْ‌غَرَ يَطَوْكُواْ عَݣُوتِنْ اللَّهْ دَغَ غِدَنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ ذُوَا عُرُوشَلِيمَ بِرْنِنْ دَاوُدَ تَرٜىٰدَ ضَوَ دَ كِطِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.