2 Samuel 6:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَأَمْسَ وَ مِكَلْ يَثٜىٰ «نَيِ ضَوَ دُواْمِنْ إِنْ‌غِرْمَمَ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ، وَنْدَ يَذَاٻٜىٰنِ أَمَيْمَكُوانْ بَابَنْكِ كُواْ وَنِ دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ غِدَنْسَ دَ يَسَانِ سَرْكِے عَكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ جَمَعَرْ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَنْيِ تَرَوَ دُواْمِنْ إِنْ غِرْمَمَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya ce wa Mikal, “Ai, na yi wannan a gaban Ubangiji wanda ya zaɓe ni a madadin mahaifinki da iyalinsa, ya naɗa ni in zama Sarkin Isra'ila, wato jama'ar Ubangiji. Lalle zan yi rawar farin ciki a gaban Ubangiji.