2 Samuel 7:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَا كَسَنْثٜىٰ تَرٜىٰدَكَيْ كُواْعِنَ دَ كَتَڢِے، نَا كُمَ كَوَرْدَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكَ دُكَ؞ بَنْدَ حَكَمَا، نَا سَا كَيِ بَبَّنْ سُنَ كَمَرْ سُونَيٜىٰنْ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰ عَدُونِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.