2 Samuel 8:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَكَامَ مَاسُ هَوَنْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ نَسَرْكِنْ ذُوابَ دُبُو طَيَ دَ طَرِے بَݣَويْ دَ سُواْجُواْجِنْ ڧَڢَا دُبُو عَشِرِنْ؞ دَاوُدَ يَغُرْغُنْتَ دُكَنْ دَوَكِنْ، سَيْدَيْ يَبَرْ دَوَكِ مَاسُ جَنْ كٜىٰكُنَ غُدَا طَرِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.