2 Samuel 9:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ظِبَ يَأَمْسَ وَ سَرْكِے يَثٜىٰ «بَاوَنْكَ ذَيْ عَيْكَتَ دُكَنْ أَبِنْدَ مَيْغِرْمَ سَرْكِے يَعُمَرْثٜىٰشِ؞» سَيْ مٜىٰڢِبُواْشٜىٰتْ يَدِنْ‌غَ ثِنْ عَبِنْثِ عَتٜىٰبُرِنْ سَرْكِے دَاوُدَ كَمَرْ سَوْرَنْ یَیَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ziba ya amsa wa sarki, ya ce, “Baranka zai yi dukan abin da sarki ya umarta.” Mefiboshet kuwa ya riƙa cin abinci a teburin sarki kamar ɗaya daga cikin 'ya'yan sarkin.