2 Samuel 9:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، أَݣَويْ وَنِ مَيْيِ وَغِدَنْ طَالُوتَ حِدِمَ مَيْ سُونَ ظِبَ؞ عَكَ كِرَا شِ، يَكُوَ ذُواْ وُرِنْ دَاوُدَ؞ سَيْ سَرْكِے دَاوُدَ يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «كَيْ نٜىٰ ظِبَ؟» ظِبَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «عِ، نِنٜىٰ، رَنْكَيَدَطٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?” Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”