2 Samuel 9:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَتَمْبَيٜىٰشِ يَثٜىٰ «بَابُوَنْدَ يَرَغُ عَثِكِنْ غِدَنْ طَالُوتَ دَ ذَنْ نُونَ مَسَ أَلْحٜىٰرِ يَدَّ اللَّهْ يَكٜىٰيِ؟» سَيْ ظِبَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «عِ، أَݣَويْ وَنِ طَنْ يُواْنَتَنْ وَنْدَ شِے غُرْغُ نٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah. Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”