2 Thessalonians 2:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، یَنْعُوَ، سَيْ كُڟَيَ دَ ڧَرْڢِے، كُكُمَ رِڧٜىٰ كُواْيَرْوَرْ نَنْ دَ مُكَ بَاكُ، كُواْ تَمَغَنَ، كُواْ تَوَسِيڧَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka'idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.