3 John 1:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Abokina ƙaunatacce, kada ka yi koyi da abin da yake mugu sai dai abin da yake nagari. Duk mai yin abin da yake nagari daga Allah yake. Duk mai yin abin da yake mugu bai taɓa sanin Allah ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا أَبُواْكِينَ وَنْدَ نَكٜىٰ ڧَوْنَ، كَدَ كَبِے مُوغُنْ غُرْبِے، أَمَيْمَكُوانْ حَكَ، كَبِے غُرْبِنْ كِرْكِ؞ دُكْ مَيْ عَيْكِنْ كِرْكِ نَ اللَّهْ نٜىٰ، عَمَّا مَيْ عَيْكِنْ مُغُنْتَا كُوَ بَيْسَنْ اللَّهْ بَ كُواْ كَطَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ƙaunataccena, kada ka kwaikwayi mugun aiki, sai dai nagari. Kowa da yake aikin nagari na Allah ne. Mai mugun aiki kuwa bai san Allah ba sam.