Acts 10:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَثٜىٰ «وَنِ بَبَّنْ سُواْجَنْ رُواْمَ نٜىٰ، مَيْ سُونَ كُواْنٜىٰلِيُسْ، يَعَيْكٜىٰمُ؞ شِ مُتُمْ مَيْ أَدَلْثِے نٜىٰ، مَيْ ڟُواْرُوانْ اللَّهْ ، وَنْدَ دُكْ جَمَعَرْ يَهُودَاوَا سُكٜىٰ ڢَطِنْ أَبِنْ كِرْكِ عَكَنْسَ؞ شِينٜىٰ وَنِ مَلاَىِٕكَ مَيْ ڟَرْكِے يَعُمَرْثٜىٰشِ يَعَيْكُواْ كَجٜىٰ غِدَنْسَ، يَجِ أَبِنْدَ ذَاكَثٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka ce, “Wani jarumi ne, wai shi Karniliyas, mutumin kirki, mai tsoron Allah, wanda duk jama'ar Yahudawa suke yabo, shi ne wani tsattsarkan mala'ika ya umarce shi, ya aiko ka je gidansa, ya ji maganarka.”