Acts 10:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُنْ سَنْ سَڧُوانْدَ يَعَيْكُواْوَ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، أَنَبَاسُ لَابَرِ مَيْ دَاطِے نَسَلَمَ تَوُرِنْ عِيسَىٰ أَلْمَسِيحُ ، شِينٜىٰ كُوَ عُبَنْغِجِنْ كُواْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah ya aiko wa Isra'ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.