Acts 12:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ غَرِ يَوَايٜىٰ، بَا ڧَرَمَرْ رُوطَرْوَ ثٜىٰ تَتَاشِ ڟَكَانِنْ سُواْجُواْجِنَّنْ بَ، عَكَنْ أَبِنْدَ يَسَامِ بِتْرُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da gari ya waye kuwa ba ƙaramar rigima ce ta tashi tsakanin sojan nan ba, kan abin da ya sami Bitrus.