Acts 12:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ هِرُدُسْ يَكَامَ بِتْرُسْ، يَسَا شِ عَكُرْكُكُ أَ حَنُّنْ سُواْجُواْجِ غُواْمَشَا شِدَ سُيِ غَادِنْسَ؞ يَنَ دَ نِيَّ يَكَٰوُاْ شِ غَبَنْ جَمَعَ يَحُكُنْتَ شِ بَايَنْ بِكٍ ڧٜىٰتَرٜىٰوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama'a bayan idin.