Acts 13:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَايِنْ دَ يَحْيَى يَكُسَ غَمَ عَيْكِنْسَ، سَيْيَثٜىٰ، ‹وَ كُكٜىٰ ڟَمَّنِ نَكٜىٰ؟ بَ ڢَا نِنٜىٰ شِ طِنَّنْبَ؞ عَمَّا أَݣَويْ مَيْ ذُوَا عَبَايَنَ، وَنْدَ كُواْ إِغِيَرْ تَاكَلْمَنْسَ مَا بَنْ إِسَ إِنْ كُنْثٜىٰبَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’